Adama Barrow ya canza sunan kasar Gambiya

Adama Barrow ya canza sunan kasar Gambiya

Shugaban kasan Gambiya, Adama Barrow, ya sha alwashin canza hukumar liken asirin kasar kuma yayi alkawarin tabbatar da yancin yan jarida a kasar.

Adama Barrow ya canza sunan kasar Gambia
Adama Barrow ya canza sunan kasar Gambia

Barrow, ya bayyana wannan ne a hira da yan jarida na farko tun lokacin da ya dau ragamar mulki a ranan Alhamis.

Baroowa ya sanar da cewa zai canza sunan hukumar liken asirin kasar wato National Intelligence Agency (NIA), wacce ake tuhume da take yancin dan adam na mutane karkashin tsohon shugaban kasan Yahya Jammeh.

KU KARANTA: Donald Trump ya fara cika alkawuransa

Sabon shugaban kasan yace kasar Gambia,wacce kasha 90 cikin 100 na mutanen kasan mabiya addinin Islama ne, sauran kuma kiristoci, kasa ce, ba kasar Islama.

Jammeh wanda shugabanci kasa na tsawon shekaru 22 ya canza sunan kasar zuma kasar musulunci a shekarar 2015. Ya sauka a mulki ne bayan ya fadi zabe a ranan 1 ga watan Disamba.

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel