Ra'ayi: Babban mai wa'azi da mata 90 ya rasu mai shekaru 93

Ra'ayi: Babban mai wa'azi da mata 90 ya rasu mai shekaru 93

- Allah yana bayyana cikin Suuratu Nisaa acikin Al-Qur'iani cewa idan miji yake so ya auri mata 2, 3 ko 4, amma idan yana jin tsoron ba zai iya yi adalci ba, guda daya yayi

- Akwai wani mutumi dan yankin Arewa mazauni jihar Niger mai suna Alhaji Mohammed Bello Masaba da mata 90 fiye da hudu

- Rahotanni na nuna cewa ya rasu dan shekara 93

Jama'a, addinin Musulunci ko Islaam, addinin adalci da tarbiya ne. Idan mutum yana da niyyar aure, yakamata ya tambaya mahaifinsa da kuma malamansa kan shari'ar aure.

Ku kalli hoton marigayi da matansa a kasa

Ra'ayi: Babban mai wa'azi da mata 90 ya rasu mai shekaru 93
Ra'ayi: Babban mai wa'azi da mata 90 ya rasu mai shekaru 93

Amma dubun matasa a yanzu suna yi kuskurai sosai bisa maganar aure. Meyesa? Wasu matasan Musulmi, basu da aikin hannu, amma suna so aure. Daga inna zasu samu kudin abinci da kaya da iri-irin abubuwa zasu saye na iyalinsu, musamman matan aure.

KU KARANTA KUMA: Kwana sun kare: Mai mata 97 ya kwanta dama

Akan auren marigayi Alhaji Masaba da mata 90 ko fiye da 90. Kuma ana cewa Masaba ya mutu yana da mata kusan 100. Irin-wannan, ba addinin Musulunci bane, domin Manzon Allah kawai ne Allah ya bayar umarnin yayi aure fiye da mata 4. Daga inna mai mata da yawa ya samu hujjarsa?

Saboda haka, idan mutum yana so yi sabuwar aure bayan matanshi sun cika 4, wani abu zai yi shine zai saki mai rashin tarbiyya acikinsu ko zai manta da sabuwar aure. Ma'ana, zai yi hakuri da dukkansu.

Muna rokon Allah kan al'amurranmu. Allah ya kara mana hasken Islam da kuma Allah ya shirya masu rashin fahimtar addinin Musulunci acikin Musulman duniya, amin.

Ku kalli wannan bidiyo kuma:

Asali: Legit.ng

Online view pixel