An kai gwamnatin tarayya da rundunar sojin sama kara bisa jefa bom a sansanin 'yan gudun hijira

An kai gwamnatin tarayya da rundunar sojin sama kara bisa jefa bom a sansanin 'yan gudun hijira

- Wasu gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu 9 na shirin kai gwamnatin tarayya da rundunar Sojin Sama kara kan jefa Bam da jirgin yaki ya yi kan sansanin 'yna gudun hijira a jihar Borno

- Kungiyoyin na bukatar gwamnatin ta biya diyyar da ta kai kimanin naira miliyan 500 ga iyalan mamatan

An kai gwamnatin tarayya da rundunar sojin sama kara bisa jefa bom a sansanin 'yan gudun hijira
Femi Falana ne ke jagorantar shigar da karar a madadin kungoyiyin

Kimanin kungiyoyin kare hakkin dan Adam guda tara ne da taimakon Femi Falana ke aniyar gurfanar da gwamantin tarayya da kuma rundunar sojin sama a gaban kotu bayan da wani jirgin sama mallakar rundunar sojin saman Najeriya da jefa bom a wani sansanin 'yan gudun hijira a Rann da ke jihar Borno.

Jaridar The Punch ta rawaito cewa, kungiyoyin da su ka hada da Centre for Women, Youth and Community Action, da the Civil Society Coalition on Transparency, Accountability and Good Governance, da the Justice and Rights Initiative, da Campaign for Democracy, da kuma the International Centre for Peace Charities and Human Development, na daga cikin kungiyoyin da ke shirin gurfanar da rundunar sojin saman Najeriya a kotu

Kawo yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane 234 sanadiyyar jefa bom din bisa kuskure da ya faru a ranar 17 ga watan Janairu a yayin da wasu da dama ke jiyya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da jefa bom a sansanin yayin da a ka kafa kwamitin bincike don gano musabbabin afkuwar lamarin.

A sakamakon haka, hukumar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta biya diyya ga wadanda abin ya ritsa da su.

An ce babban lauya mai lambar kwarewa ta SAN wanda ke kare hakkin dan Adam, Femi Falana ne zai tsaya wa kungiyoyin ba tare da ko kwabo ba.

Rahoton ya ambato Falana ya na cewa:

"Na kudiri aniyyar shiga lamarin ba tare da ko kwabo ba. Za mu fara da gano mutane nawa ne a ka kashe.

"Rundunar sojin sama ta ce mutum 60 ne abin ya rutsa da su bayan an binne mutum 236. Abu na 2 za mu binciko lamarin kuskure ne ko kuwa da gangan ne."

A bangaren sa,. babban daraktan Centre for Women, Youth and Community Action, Nawani Aboki cewa ya yi:

"Mu na shirye-shiryen rubuta korafi zuwa ga gwamnatin tarayya don a biya diyya tare da goyon bayan kasashen duniya, saboda in mu ka bar abin a cikin gida gwamanti ba za ta dauke shi da muhimmanci ba".

"Za mu fara da korafin mu kuma wuce har matakin majalisar dinkin duniya sannan mu sanar da al'ummar duniya abin da ke faruwa a Najeriya, mu kuma sa gwamnati ta biya diyya ga duk wadanda a ka kashe.

"Matakin farko shi ne tabbatar da yawan mutanen da su ka mutu. Mutane su na magana kan abin da ba su sani ba. Mutane nawa ne su ka mutu sanadiyyar bom din? Ta haka ne za mu gane diyyar nawa za mu nema."

"Idan mu ka ce biliyan 500, amma mu ka samu mutane da yawa sun mutu, ya za mu yi? Saboda haka mu na bukatar mu shirya mutane don gano yawan wadanda su ka mutu a sanadiyyar bom din sannan mu duba mu ga nawa ya kamata a biya a matsayin diyya ga iyalan wadanda su ka mutu."

Shi ma da ya ke magana shugaban kungiyar the Campaign for Democracy, Mista Bako Abdul Usman, cewa ya yi kungiyoyin su na bukatar naira biliyan 500 a matsayin diyya.

Ku cigaba da bin mu a Facebook a http://www.facebook.com/naijcomhausa

da kuma a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel