Dalilin da yasa Buhari ba zai iya magance matsalar Najeriya ba – Balarabe Musa yayi magana

Dalilin da yasa Buhari ba zai iya magance matsalar Najeriya ba – Balarabe Musa yayi magana

- Balarabe Musa yace Buhari bazai iya magance matsalolin Najeriya ba

- Shugaban dattawan yace shugaban kasar baida isashen karfin da zai magance al’amuran kasar

- Sannan ya shawarci shugaban kasa da ya fara shirin sabonta zamantakewa

Dalilin da yasa Buhari ba zai iya magance matsalar Najeriya ba – Balarabe Musa yayi magana
Balarabe Musa

Abdulkadir Balarabe Musa ya kasance tsohon gwamnan jihar Kaduna a lokacin jumhuriyar Najeriya ta biyu.

A baya Shugaban dattawan yaki yin sharhi a kan halin da kasar ke ciki, amma a wani hira da yayi tare da jaridar Vanguard kwanan nan, yay i korafi game da karfin Buhari gurin magance mastalolin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Imam ya bukaci yan Najeriya da suyi ma Buhari addu’a

Yace: “Shugaban kasar ya kasance kamar wanda ya amshi mulki daga hannunsa. Idan na tambaye ku bambancin sa da wanda ya karbi mulki daga hannun sa. Babu bambanci.

“Dukkan su sun yarda da tsarin ra’ayin kai tukuna, yayinda ra’ayin jama’a ke biyo bayan nasu. Baida isashen karfin da zai magance halin dake cikin Najeriya.”

Mista Musa ya zargi gwamnati mai ci yanzu da ta bar tattalin arziki a kamfanoni masu gashin kansu sannan kuma ta bari suke yanke abunda ke faruwa, ya kara da cewa wannan ba zai kasar ko ina ba.

Daga karshe, tsohon gwamnan ya shawarci Buhari da ya fara sabonta zamantakewar Najeriya nan da nan, tare da daukan jagorar tattalin arziki da kuma kawo tsarin da zai sa ra’ayin mutane sama da na kowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel