Sabon hoto ya tabbatar da cewa shugaban kasa Buhari na raye kuma cikin koshin lafiya a Landan

Sabon hoto ya tabbatar da cewa shugaban kasa Buhari na raye kuma cikin koshin lafiya a Landan

An saki wani sabon hoto na shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayinda yake jin dadin hutunsa a birnin Landan.

Sabon hoto ya tabbatar da cewa shugaban kasa Buhari na raye kuma cikin koshin lafiya a Landan
Shugaban kasa Buhari na hira tare da Aisha Alubankudi da Gwamna Ibikunle Amosun

Wata mai amfani da shafin Facebook Aishat Alubankudi ce ta buga hoton a yammacin ranar Juma’a, 27 ga watan Janairu bayan wani ganawa da shugaban kasar Najeriya.

Ta rubuta wani dan takaitaccen bayani tare da hoton wanda ya nuna gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun, wani makusancin shugaban kasa, zaune a wani kujera dake kallon na shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Imam ya bukaci yan Najeriya da suyi ma Buhari addu’a

Alubankudi ta kasance yar Najeriya kuma mai shafin rubutu wacce ke zaune a birnin Landan kuma makusanciyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ta kuma rubuta wani dan takaitaccen furuci tare da hoton da saki wanda aciki ne ta roka ma wadanda ke cewa shugaban kasa yam utu gafara daga Ubangiji.

Ta rubuta: “Hoton PMB a yau. Allah ya gafarta ma wadanda ke ikirarin cewa yana cikin injin din taimako a asibitin Kings College. Baba dariji won nitori won o moo un ti won nse (wani ya fassara)” wato dai Allah ya yafe musu domin basu san abunda suke yi ba.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa na zagi shugaba Buhari, Sanata Shehu Sani yayi magana

Wannan ya kasance hoto na biyu dake tabbatar da cewa shugaban kasar na raye kuma cikin koshin lafiya a kwanaki uku da suka wuce fadar shugaban kasa ta saki hoton shugaban kasar yana kallon Channels TV shirin Sunday Politics a ranar Litinin, 23 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel