Trump zai gina katanga tsakanin Amurka da Mexico

Trump zai gina katanga tsakanin Amurka da Mexico

– Sabon Shugaban Kasar Amurka ya fara shirin gina katanga tsakanin Amurka da Mexico

– Trump ya sa kafar wando daya da bakin haure

– Donald Trump kuma ya fara shirin gina katangar karfe tsakanin sa da makwabta

Trump zai gina katanga tsakanin Amurka da Mexico
Trump zai gina katanga tsakanin Amurka da Mexico

Kamar yadda aka sani sabon shugaban Kasar Amurka, Donald Trump ya sha alwashin kare iyakokin Kasar Amurka daga bakin haure. Yanzu haka Trump ya bada umarnin a fara shirin gina katuwar katanga tsakanin Kasar Amurka da Kasar Mexico masu makwabtaka da juna.

Trump dai yayi alkawarin kare Amurka daga masu shigowa su tare a Kasar ba a san da su ba. Idan ba a manta ba yanzu haka dai har Trump ya fatattako ‘Yan Afrika kusa 100 gida. Haka kuma Shugaba Trump ya hana wasu Kasashen Musulmi shigowa Kasar ta Amurka

KU KARANTA: Shugaban Kasar Gambia ya koma gida

Trump ya fada lokacin neman zabe cewa Amurka za ta gina katanga tsakanin ta da Mexico mai nisan miles 2000, kuma Kasar Mexico ce za ta biya kudin aikim. Sai dai Shugaban Kasar Mexico Pena Nieto yace Kasar Mexico ba za ta biya ko sisi wajen wannan aiki ba.

Shugaban Kasar Mexico dai yace Kasar sa ba ta yarda da gina katanga tsakanin ta makwabta ba. Sai dai ba a sani ba Shugaban Kasar Mexico zai gana da Trump din.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel