Iya kudin ka-iya shagalin ka! Sarkin Kano yayi watsi da dokar auren Danbatta

Iya kudin ka-iya shagalin ka! Sarkin Kano yayi watsi da dokar auren Danbatta

- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya yi watsi da wata doka da majalisar fadar Dambatta ta kafa wadda ta kayyade sadakin auren mata a garin.

- Dokar ta kayyade kudin zance na al'ada a kan kada ya haura 20,000, sannan mafi karancin sadaki 20,000, haka kuma ta kayyade adadin kayayyakin da za a rinka sanya wa a kayan lefe.

Iya kudin ka-iya shagalin ka! Sarkin Kano yayi watsi da dokar auren Danbatta
Iya kudin ka-iya shagalin ka! Sarkin Kano yayi watsi da dokar auren Danbatta

Amma Sarki Sanusi ya ce hakan ba abin da zai jawo sai dai a dinga auren mata ana sakinsu a duk lokacin da aka ga dama domin "an ga sun yi arha".

Ya ce, ''Ba za mu yarda da wannan tsari ba don ba don haka aka ajiye shari'ar aure ba, wanda yake da halin kashe kudi da yawa ya yi, wanda ba shi da hali ya yi daga cikin abin da Allah ya ba shi.''

Sarkin ya kara da cewa, "Bai kamata ku hana wa mata arzikinsu da Allah ya basu ba, idan yarinya ta samu mai sonta ko akwati 10 ya ga zai mata a bar shi ya yi."

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta kusa bankwana da dauke wuta - Fashola

Ya yi kira ga majalisar hakimin Dambattan da cewa kamata ya yi su kafa kwamiti kan yadda za a dinga gyaran aure da magance matsalolinsa kamar na dukan mata da sauran su, don su ne suka fi zama ruwan dare.

"Kullum sai an kawo mana shari'ar dukan mace a nan, bayan kuwa Musulunci bai bayar da wannan damar ba, don haka kamata ya yi ku yi gyara a kan haka.

Sakin mata barkatai da auren dole da dukan mata da barin yara barkatai da cire yara kanana daga makaranta a aurar da su, su ne matsalolinmu ba wai sadakin 20,000 ba," in ji Sarki Sunusi.

A farkon watan Janairu ne dai masu fada aji a Dambatta suka fitar da wani kundin doka wanda ya takaita yawan wahalhalun da ake yi wajen aure.

Dama dai a farkon saka dokar sai da matan garin suka koka amma samarin karamar hukumar bakinsu har kunne domin sun ce abin da suka dade suna jira ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel