Dakarun ECOWAS sun fallasa shirin kashe shugaba Adama Barrow da Jammeh ya shirya

Dakarun ECOWAS sun fallasa shirin kashe shugaba Adama Barrow da Jammeh ya shirya

Dakarun sojoji kungiyar kawancen kasashen Afrika na yamma, ECOWAS, sun bada rahoton bacewar wasu tarin makamai da alburusai daga fadar gwamnatin kasar Gambia dake Banjul, babban birnin kasar ta Gambia.

Dakarun ECOWAS sun fallasa shirin kashe shugaba Adama Barrow da Jammeh ya shirya
Dakarun ECOWAS sun fallasa shirin kashe shugaba Adama Barrow da Jammeh ya shirya

Dakarun Sojin sunce an nemi wadannan makamai a inda aka saba ajiye sama ko kasa amma ba gan su ba.

Buguwa da kari, wata jaridar kasar mai suna ‘The Point’ ta bayyana cewar dakarun sojin sun gano cewar an zuba wasu sinadarin guba a na’urorin sanyaya dakunan, wato AC dake dukkanin dakunan fadar shugaban kasar wadanda ka iya hallaka yan cikin dakunan.

KU KARANTA: Yan Najeriya sun yi jimamin mutuwar wata jarumar Soja mace

Ana zargin cewar tsohon shugaban kasar mai murabus Yahaya Jammeh ne ya shirya wannan shirin don hallaka sabon shugaban kasar Adama Barrow.

Jaridar ta kara da cewa a yanzu haka dakarun ECOWAS suna binciken jami’an tsaron fadar shugaban kasar don samun bahasin lamarin. ana tunanin binciken da ake gudanarwa ya kawo tsaikon fara gudanar da mulki na sabon shugaba Barrow.

Dama dai bayan tserewar Yahya Jammeh daga kasar ne aka samu rahoton cewar ya tattara motocin fadar shugaban kasar na alfarma da makudan miliyoyin daloli ya gudu dasu, sa’annan an ruwaito suma jami’an sojojin fadar sun sace kwamfutoci da sauran kayan alatu dake jibge a fadar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli bidiyon rantsar da sabon shugaban kasar Gambia Adama Barrow a nan:

Source: Legit

Tags:
Online view pixel