YANZU-YANZU! Yau Adama Barrow zai koma gida

YANZU-YANZU! Yau Adama Barrow zai koma gida

A yau Alhamis ne shugaban Gambia Adama Barrow zai koma Banjul fadar gwamnatin kasar, bayan kawo karshen rikicin siyasar kasar da har ta kai ga rantsar da shi a Senegal.

YANZU-YANZU! Yau Adama Barrow zai koma gida
YANZU-YANZU! Yau Adama Barrow zai koma gida

Rahotanni sun ce dakarun Afrika 4,000 ke cikin Gambia yanzu haka wadanda za su kare lafiyar shugaban da tabbatar da zaman lafiya, yayin da wasu rahotanni ke cewa sojojin haya sun shiga kasar dauke da muggan makamai bayan ficewar Yahya Jammeh.

Da misalin karfe 4 na yammacin goben ne a gogon kasar, Adama Barrow zai shiga Banjul kamar yadda wani na kusa da shi Mai Fatty ya tabbatar.

ECOWAS ce ta bukaci Barrow ya gaggauta komawa gida bayan ficewar Jammeh domin tunkarar matsalolin kasar musamman tattalin arziki da kuma tsaro.

Wani batu na farko da ake ganin shugaba Barrow zai magance, shi ne rikicin cikin gida da ya kunno kai kan zaben mataimakiyarsa Fatouma Jallow wacce ta haura shekarun da kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade.

Sannan kuma barazanar tsaro da ke gaban Barrow musamman wasu rahotannin da suka ce an shigo da muggan makamai a cikin Gambia da kuma ‘yan daba da ba su jin ingilishi da harshen Wolof da mutanen Gambia mafi yawanci ke magana da shi.

Yanzu haka dakarun ECOWAS na gudanar da bincike tare tabbatar da tsaro kafin isowar shugaba Adama Barrow.

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel