Jam’iyyar APC ta cire Soludo daga ‘Yan takarar ta?

Jam’iyyar APC ta cire Soludo daga ‘Yan takarar ta?

– ‘Yan takara 13 suka fito takarar gwamnan jihar Anambra a karkashin Jam’iyyar APC

– Tsohon gwamnan CBN, Farfesa Charles Soludo yace ba zai tsaya takara a karkashin APC ba

– Karshen shekarar nan za ayi zaben gwamna a Anambra

Jam’iyyar APC ta cire Soludo daga ‘Yan takarar ta?
Jam’iyyar APC ta cire Soludo daga ‘Yan takarar ta?

A jiya muka kawo labarin cewa kusan Mutane 13 suke neman tikitin tsayawa takarar kujerar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC a Jihar Anambra a zabe mai zuwa. Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar, Mista Emeka Ibe ya bayyana haka.

To sai dai yanzu majiyar mu sun nuna cewa Farfesa Soludo tsohon Gwamnan babban Bankin Najeriya na CBN yace babu shi a cikin ‘Yan takarar. Farfesa Soludo yace shi ba dan Jam’iyyar APC bane don haka babu yadda za ayi ya tsaya takara a karkashin Jam’iyyar.

KU KARANTA: Ya kamata Inyamurai su yi mulki inji OBJ

Za dai ayi zaben sabon Gwamnan Jihar ne a Nuwamban bana. Jam’iyyar APC tana kokarin karbe mulki daga hannun Gwamna Willie Obiano na Jam’iyyar APGA. Gwamna Okorocha na Imo yayi kira ga Inyamurai da su shigo jirgin APC a karshen wancan makon.

Sauran masu neman kujerar sun hada da Sanata Andy Ubah da Sanata Uche Ekwunife. Sannan akwai Cif Paul Chukwuma, Cif Obinna Uzor, Tony Nwoye, Prince D. Okonkwo da Cif George Muoghalu. APC dai tace za ta bari duk wanda ya iya allon sa ya wanke.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel