Yanzu Yanzu: Boko Haram ta kashe mutane 8, ta sace mata 7 a yayin kaddamar da wani hari a jihar Barno

Yanzu Yanzu: Boko Haram ta kashe mutane 8, ta sace mata 7 a yayin kaddamar da wani hari a jihar Barno

Kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ya sake kai wani hari a karamar hukumar Askira Uba na jihar Borno inda ta kashe mutane 8 tare da sace mata 7.

Yanzu Yanzu: Boko Haram ta kashe mutane 8, ta sace mata 7 a yayin kaddamar da wani hari a jihar Barno

Jaridar Punch ta ruwaito harin ya faru ne a kauyen Dzaku a daren Litinin 23 ga watan Janairu. Majiyar mu ta shaida mana cewar mayakan Boko Haram sun shigo kauyen nasu da tsakar dare a cikin wasu motoci kirar Hilux guda biyu dauke da bindigun AK-47 da bamabamai na gargajiya.

Wani mazaunin kauyen, Amos Ali ya bayyana mana cewar kanwarsa na daya daga cikin matan da aka sace.

KU KARANTA: Za’a fara yi ma Fulani makiyaya rajista a iyakokin kasar nan

Yace “saboda rashin waya, yan kauyen basu samu damar kirar mu don shaida mana harin ba a ranar Talata, sun kashe mutane 8, tare das ace mata 7, ciki har da kanwata. Mu dai wannan lamari na damun mu, musamman yadda sojoji suke fadin sun murkushe yayan Boko Haram.

Amma har zuwa yanzu hukumar yansandan jihar bata tabbatar da labarin kai harin ba. Ita ma jaridar The Nation ta ruwaito cewar mutane uku kadai aka kashe sakamakon harin na kauyen Dzako, inda ta ruwaito wani mazaunin garin Askira Uba ma i suna Ibrahim Askira yana fadin:

“a yanzun nan da nake tattaunawa da kai, mutane da dama sun tsere zuwa cikin daji, ba zan iya tabbatar maku da adadin mutanen da suka sace ba.”

Shima wani mafarauci mai suna Aminu ya cigaba da fadin “jama’an kauyen nan a rikide suke sakamakon harin nan, bama iya yin bacci, don haka nake kira ga jami’an tsaro su karfafa tsaro a kauyen mu, idan ba haka kuwa Boko Haram zata gama damu gabaki daya.”

A wani labarin kuma, kimanin mutane uku ne aka tabbatar da mutuwarsa a wasu hare haren kunar bakin wake guda biyu da suka faru a garin Maiduguri a ranar Laraba 25 ga watan Janairu da sanyin safiya, a cewar jami’an tsaro.

Rahotannin sun nuna cewa daba dan kokarin jami’an tsaro ba, da an samu mamata da wadanda zasu jikkata da dama.

Allah ya kiyaye gaba, amin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel