FG ta samu ton taki 800,000 daga kasar Maroko, zata sayar da buhu N5,000

FG ta samu ton taki 800,000 daga kasar Maroko, zata sayar da buhu N5,000

Takardan yarjejeniya da gwamnatin tarayya da kasar Maroko suka yin a hada takin noma yayinda kasar Maroko na shirin turo taki noma NPK zuwa Najeriya.

FG ta samu ton taki 800,000 daga kasar Maroko, zata sayar da buhu N5,000
FG ta samu ton taki 800,000 daga kasar Maroko, zata sayar da buhu N5,000

Gwamnatin tarayya tace bisa ga matsalan a manoma ke samu na tsadan taki, tayi aiki domin saukaka yadda manoma zasu samu taki a kudi N5,000 ga buhu sabanin N10,000 da ake sayarwa a yanzu.

Ministan aikin noma da raya karkara,Cif Audu Ogbeh,ya bayyana wannan ne a jiya,yayinda ayke hira da maneman labarai akan wannan sabuwar abu da ma’aikatar zatayi domin tabbatar da kyan abinci.

Game da cewarshi: “ Sinadarin Phosphate zai fara zuwa a wanan mako, yayinda zamu fara hadawa da wuri.”

KU KARANTA: Kotu tace ta dade da bayar da belin Dasuki

Ya tabbatar da cewa wannan abu da za’ ayi zai rage kudin buhun taki a kasuwa daga N10,000 zuwa N5,000.

“Idan aka fara hadawa, yayinda ake tattaunawa., kudin takin zai sauko. Zamu tabbatar da cewa kowani kamfanin hada taki a kaa ta samu abinda take bukata, duk da cewan mashinan hadawan na da karanci.

“Ba Najeriya kadai muke baiwa taki ba; muna baiwa makwabtan kasashe wadanda ke zuwa muke san musu, ba zamu iya hanasu ba, amma wajibi ne mu koshi tukunna,”

Yayinda yake Magana akan sabon na’urar aikin, ministan yace : “ Dalilin da yasa shine tabbatar da cewa hada abinci bai shafi koshin lafiyan mutanen kasa ba."

Kana kuma ministan ya nuna damuwarsa akan tashn cutan koda da hanta da ke samuwa a matasa da yara.

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel