To fa! Manyan sojojin sun mutu a hadarin jirgin sama

To fa! Manyan sojojin sun mutu a hadarin jirgin sama

- Sojojin Kamaru hudu tare da babban sojin da ke jagorantar yaki da kungiyar Boko Haram sun rasa rayukansu bayan da jirgin saman da suke ciki ya yi hadari a arewacin kasar.

- Ministan sadarwa na kasar Issa Tchiroma Bakary, ya ce Janar Jacob Kodji da wasu sojoji uku da suka hada wani Kanar ne suka mutu a hadarin.

To fa! Manyan sojojin sun mutu a hadarin jirgin sama
To fa! Manyan sojojin sun mutu a hadarin jirgin sama

Sai dai bai yi cikakken bayani kan musabbabin hadarin ba, wanda ya faru a kusa da kan iyakar kasar da Najeriya.

Wata majiyar soji ta ce, "suna gudanar da aikinsu ne a yankin gandun daji na Waza a wani bagare na yakin da suke yi da Boko Haram."

Janar Kodji ne jagoran Emergency 4, sunan da aka bai wa daya daga cikin rundunonin da Kamaru ta kaddamar domin yakar Boko Haram.

Dakarun Kamaru sun matsa lamba wurin hare-haren da suke kai wa Boko Haram tun bayan da Najeriya ta ce ta kori mayakan daga sansaninsu da ke dajin Sambisa.

Janar Kodji shi ne janar din sojin Kamaru na farko da ya mutu a yakin na Boko Haram.

Nan gaba a ranar Litinin ne ake sa ran kai gawar sojojin zuwa Yaounde, babban birnin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel