An rasa minista a Najeriya

An rasa minista a Najeriya

– Wani tsohon Ministan Najeriya ya rasu yanzu nan

– Alhaji Saka Sa’adu ya rasu yana da shekara 79

– Saka Sa’adu ya rike Ministan Ilmi a baya

An rasa Minista a Najeriya
An rasa Minista a Najeriya

Jaridar Punch ta rahoto cewa an yi rashin wani tsohon Ministan Najeriya. Alhaji Saka Sa’adu ya rasu a Asibitin horar da aikin Likitoci da ke Garin Ilorin na Jihar Kwara. Tsohon Ministan ya dai rasu ne a yau Litinin.

Alhaji Abdulkadir Sa’adu wani Dan Marigayin ya bayyana haka. Alhaji Abdulkadir yace mutuwar fuji’a ce kurum ta dauke Mahaifin na sa. Abdulkadir Sa’adu ya bayyana cewa Mahaifin sa ya bar Duniya yana da shekaru 79.

KU KARANTA: An yankewa Dan Najeriya hukuncin dauri a Kasar waje

Sa’adu asalin Dan Garin Okekere ne na Jihar Kwara. Ya rike Ministan Ilmi na Kasar a can baya. Za kuma a birne sa a yau da karfe 4:00 na Yamma bayan gidan Gwamnatin Jihar Kwara

Yanzu kuma muke samun labarin cewa wani jirgin Kasar Kamaru mai fada da ‘Yan Boko Haram ya kife, inda wasu Sojoji suka rasa rayukan su. A ciki dai akwai wani babban Janar na Soji da ya rasu.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel