Cigiya: Ana neman yan’uwan wasu mutane da wani mummunan hadari ya rutsa dasu a hanyar Abuja

Cigiya: Ana neman yan’uwan wasu mutane da wani mummunan hadari ya rutsa dasu a hanyar Abuja

Wani mummunar hadari ya auku a babban titin hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranan Asabar 21 ga watan Janairu, amma sai dai an gagara gano yan’uwan mutanen.

Cigiya: ana neman yan’uwan wasu mutane da wani mummunan hadari ya rutsa dasu a hanyar Abuja

Wani ma’abocin kafar sadarwar Facebook Musa Abdulkarim Itodo shine ya watsa hotuna tare da bidiyon lamarin, inda ya bayyana a ciki cewar har yanzu ba’a san yan’uwan mutanen da suka jikkata sanadiyyar hatsarin ba.

KU KARANTA:Gwamna Tambuwal ya buƙaci ýan Najeriya dasu yi ma Buhari addu’a

Musa yace “wannan hatsarin ya faru ne akan titin Abuja, nan gaba da Abaji, mutanen cikin motar sun tsira, amma fa sun samu manyan raunuka.

“Muna rokon jama’a da a watsa wannan labarin har sai yan’uwan su sun gani, don su zo su dauke su.”

Ga bidiyon mutanen a nan kamar haka:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel