Sojoji zasu mamaye kudancin Kaduna

Sojoji zasu mamaye kudancin Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya bayyana shirin samar da barikin soja a Kafanchan da Kachia, domin inganta sha'anin tsaro a yankin kudancin Kaduna.

Sojoji zasu mamaye kudancin Kaduna
Sojoji zasu mamaye kudancin Kaduna

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da yake tarbar majalisar sarakunan jihar wadanda suka ziyarci fadar gwamnan, domin jajenta masa asarar rayuka da dukiyoyin da ake fuskanta a wasu kananan hukumomi da ke kudancin jihar.

Gwamnan ya kara da cewa, babban hafsan tsaron kasa ya amince da karin bataliyar sojojin Nijeriya 2 da za a gina musu bariki a Kafanchan da Kachia, ko kuma wani waje na daban idan ba a samu damar yi a Kachia ba.

Ya ce, gwamnatin jihar ta kuma gayyato wata kungiya mai zaman kanta dake kokari kan sasanta tsakanin al'umma da samar da zaman lafiya ta Humanitarian Dialogue, wacce ta samu nasara a jihar Filato, bayan rikice rikicen da aka yi a jihar.

Ya nemi sarakunan gargajiya da sauran shugabannin al'umma su taimaka wajen kwantar da hankalin su, da ba su hakuri kan muhimmancin zaman tare cikin fahimtar juna da hadin kai.

A jawabin sa, shugaban tawagar sarakunan kuma mai martaba Sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris ya yabawa kokarin da gwamnatin jihar ke yi na ganin an samu zaman lafiya mai dorewa tare da bukatar kara karfafa matakan tsaro, domin kawo karshen salwantar da rayuka da ake cigaba da fuskanta a yankunan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel