Wata yar shekara 18 guji iyayenta bayan ta musulunta

Wata yar shekara 18 guji iyayenta bayan ta musulunta

- Habiba Ishaku 'yar kimanin shekara 18 da haihuwa ta kalubalanci iyayenta a gaban kuliya manta sabo, a jihar Katsina

- Habiba wadda asalinta ba musulma ba ce ta shigo Musulunci ne a shekarar da ta gabata, inda ta auri wani matashi mai suna Jamilu Lawan ba tare da amincewar mahaifanta ba

Wata yar shekara 18 guji iyayenta bayan ta musulunta
Wata yar shekara 18 guji iyayenta bayan ta musulunta

A zaman kotun da aka yi tsakanin Habiba da mahaifanta karkashin jagorancin kungiyar kiristoci mabiya majami'ar ECWA, iyayen nata sun kalubalanci komawar ta Musulunci, a inda suka ce Habiba yarinya ce karama kuma shekarunta 14 ba 18 ba kamar yadda ta ce, in ji mahaifinta Mr. Ishaku Tanko.

Habiba 'yar asalin karamar hukumar Kankara dake jihar Katsina ta gabatarwa mai shari'a Baraka Isiyaku Wali takardar haihuwarta da ta nuna shekarun ta 18.

Daya daga cikin abokan maihaifin Habiba ya ce basu yarda da takardar haihuwar Habiba ba saboda da harshen Hausa aka rubuta bada Turanci ba.

Umar shi ne Lauya mai kare Habiba, ya ce babu wata doka a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan da ya tanadi rubuta takardar haihuwa da Turanci, don haka tana da damar yin amfani da takardar.

Mai shari'a Baraka Iliyasu Wali ta ce, Habiba na iya yin amfani da takardar ko kuma ta sake wata, sannan ta daga shari'ar zuwa 25 ga watan Janairun da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel