Ku kiyayi kasar Libiya ko kuyi asaran rayukan ku – Fadar shugaban kasa

Ku kiyayi kasar Libiya ko kuyi asaran rayukan ku – Fadar shugaban kasa

- Gwamnatin Najeriya ta gargadi yan Najeriya masu zuwa Libiya su daina daga yanzu

- Wannan gargadi na zuwa ne daga ofishin mai taimakawa shugaba Buhari akan harkokin wajen Najeriya

Ku kiyayi kasar Libiya ko kuyi asaran rayukan ku – Fadar shugaban kasa
Ku kiyayi kasar Libiya ko kuyi asaran rayukan ku – Fadar shugaban kasa

An gargadi yan Najeriya akan zuwa kasar Libiya bisa ga rahoton cewa ana kashe bakaken fata masu shigowa kasar.

News Agency of Nigeria (NAN) ta bada rahoton cewa wannan gargadi na zuwa ne daga ofishin Abike Dabiri-Erewa, mai taimakawa shugaba Buhari akan harkokin wajen Najeriya.

An samu rahotannin cewa ana hallaka rayuwan bakaken fata masu su sia kasar kuma Abike Dabiri tayi gargadi duk da cewa bata tabbatar da labarin ba.

KU KARANTA: Muna amince da Ayo Fayose- PDP

“Ina kara kira gay an Najeriya da su guji kasar Libiya saboda idan aka kama mutum ya shiga kasar ba bisa ga doka ba, kashe shi za’ayi.

“Lokacin da nike shugaban kwamitin wajen Najeeirya a majalisar wakilai, mun sa baki a wani sha’ani inda ake son kashe yan Najeriya 24.

“Kwamitin tare da kungiyar SERAP muka rubuta kara ga majalisar dinkin duniya UN, AU da ECOWAS wanda yasa aka sake su daga baya.

“Watanni biyu da suka gabata,NEMA tare da ofishin jakadancin Najeriya a Libiya sun kwashe yan Najeriya 2000 daga Libiya.”

“Mutane Libiya na fuskanta matsalar kansu yayinda har yanzu ba wata shugabancin kwarai a kasar.”

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel