Wata mata ta haifi yan Uku a sansanin ýan gudun hijira

Wata mata ta haifi yan Uku a sansanin ýan gudun hijira

Wata mata dake zaune a sansanin yan gudun hijira a kasar Tanzania mai suna Nywandwi Velelia ta haifi jarirai guda uku a dakin haihuwa dake sansanin yan gudun hijira na Ndutu.

Wata mata ta haifi yan Uku a sansanin ýan gudun hijira
Wata mata ta haifi yan Uku a sansanin ýan gudun hijira

Zuwa yanzu Nywandai da jariran nata suna cikin koshin lafiya, kuma har an sallamo su daga asibitin.

KU KARANTA:Abin mamaki: Akuya da kwankwadar lemun kwalba (Bidiyo)

Sai dai da sauran runa akaba musamman dangane da walwalan jariran sakamakon tantin da suke ciki ya bule, yana zubar da rawa, sa’annan kuma basu da gadon kwana sai dai a kan tabarma da aka shimfida a kasa tare da iyayensu da yayyensu uku.

Mahaifiyar jariran ta bayyana damuwarta, inda tace “a gaskiya ko kayan sawa bani da shin a jarirai, don haka ina cikin damuwa.”

Mahaifiyar jariran Nyandwi na daya cikin mutane fiye da 89,000 dake zaune a sansanin yan gudun hijira na Nduta inda suke fama da lalacewar makewayi wanda hakan ke samar da cututtuka daban daban.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel