EFCC ta caji ma’aikatanta akan sanya sunayen jabun ma’aikata 50,000 cikin albashi

EFCC ta caji ma’aikatanta akan sanya sunayen jabun ma’aikata 50,000 cikin albashi

- Hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta caji ma’ aikatanta guda 5 akan sanya sunayen jabun ma’aikata 50,000 cikin tsarin albashin gwamnati

- Wata majiyar EFCC tace an kai ma’aikatan kotu duk da cewa ba’a gurfanar da su ba tukun

EFCC ta caji ma’aikatanta akan sanya sunayen jabun ma’aikata 50,000 cikin albashi
EFCC ta caji ma’aikatanta akan sanya sunayen jabun ma’aikata 50,000 cikin albashi

Hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta caji ma’ aikatanta guda 5 akan sanya sunayen jabun ma’aikata 50,000 cikin tsarin albashin gwamnati

Game da cewar jaridar Punch, wata majiyar EFCC tace an kai ma’aikatan kotu duk da cewa ba’a gurfanar da su ba tukun.

KU KARANTA: Yan shi'a sun ziyarci Bishap a Sakwwato

Wani ma’aikacin EFCC yace: “ zaku tuna cewa ma’aikatar kudi ta turo sunayen wadanda ke sanya sunan jabun ma’aikata. Man caji mutane 5 cikinsu, sauran uma ana bincike.

A yayin bincike, an samu cewa wata tsohuwar ma’aikatar gidaje da raya karkara na amsan albshi har yanzu bayan an sauya ma’aikatar zuwa hukumar binciken sararin samaniya. Mun samu cewa ya amsa albashin 9.6miliyan kuma bai daina amsan albashin tsohuwar ma’aikatar ba.

“Wannan laifin ma’aikatar ne wacce taki daina bashi albashi lokacin da ya kamata tayi. Shi kuma abin zargin nada laifin kin fadawa gwamnati."

Zaku tuna cewa mai Magana da yawun shugaban kasa, Malam Grba Shehu ya bayyana a watan Disamba cewa a ma’aikatar kudi , an gano jabun ma’aikata 50,000 wanda suke amsan N13bn kowani wata a sama.

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel