An daure wani dan Najeriya a Kasar Scotland

An daure wani dan Najeriya a Kasar Scotland

– An kama wani Dan Najeriya da laifin kisa da fyade a Ingila

– Tuni aka yanke masa hukuncin dauri

– Dan Najeriyar dai dan manya ne a can ya kuma zo karatu ne

An daure wani Dan Najeriya a Kasar Scotland
An daure wani Dan Najeriya a Kasar Scotland

An samu wani Dan Najeriya da laifin fyade da kuma kashe wata mata a can Kasar Scotland. An dai kama wannan yaro ne da laifin yi wa wata mata mai-zaman ka ta fyade, daga karshe kuma ya kashe ta.

Wannan yaro dai ya aikata wannan mummunan laifi ne jim kadan bayan zuwan sa Kasar domin karatu a Jami’ar Robert Gordon ta Birnin Abardeen. Mahaifin sa dai wakilin Najeriya ne a Kasar ta Scotland.

KU KARANTA: An kama wani dan ta'addan duniya a Najeriya

Bala Chinda mai shekau 26 dai yayi lalata da Jesica McGraa kafin ya kashe ta a shekarar bara ta 2016. Duk da ya karyata hakan, bincike ta na’urar daukar hoto na CCTV sun nuna cewa Bala ya ja Marigayiya Jesica zuwa dakin kwanan sa, wanda daga nan ba a kara ganin ta ba, sai gawar ta.

Kotu dai ta yankewa Bala Chinda hukucin daurin rai-da-rai bayan an gano cewa ya kashe wannan mata mai zaman kan ta. Watakila dai shake ta aka yi har ta mutu, ana kuma tunanin rikicin kudi ne ya hadu su.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel