Buhari bai mutu ba, inji Fadar Shugaban Kasa

Buhari bai mutu ba, inji Fadar Shugaban Kasa

– Fadar Shugaban Kasa ta musanya rade-radin cewa Shugaban Kasa ya mutu

– Wata Jaridar Metro ce ta rahoto cewa Buhari ya rasu a Ingila

– Garba Shehu ya ce Shugaba Buhari fa yana nan a raye

Buhari bai mutu ba,Inji Fadar Shugaban Kasa
Buhari bai mutu ba,Inji Fadar Shugaban Kasa

Wata Jarida mai suna Metro-UK ta rahoto cewa Shugaban Kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya samu cikawa a Ingila inda ake duba sa a wani Asibiti. Jaridar tace Shugaban Kasar na fama da wani rashin lafiya ne da ba a gane kan sa ba.

Sai dai Fadar Shugaban Kasar tayi wuf ta karyata wannan rahoto. Mai magana da bakin Shugaban Kasar, Malam Garba Shehu yace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na nan da ran sa.

KU KARANTA: Hotunan Shugaba Buhari

Har dai Garba Shehu yayi ba’a ga masu yada jita-jitar, yana mai cewa babu yadda za ayi Shugaba Buhari ya kasance a wurare biyu lokaci guda. Watau kamar dai Tsohon Shugaba Jonathan da aka ce yana Amurka, sai kuma ga shi a Jihar Ogun.

Femi Adesina, ya nemi masu yada wannan jita-jitar da su tuba. Shugaba Buhari dai ya tafi hutu Kasar Ingila a karshen wancan makon. Kuma ba dai wannan bane karo na farko da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya tafi hutu, an mika shugabancin kasar hannun Mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel