Barcelona ta karya camfin shekaru 9

Barcelona ta karya camfin shekaru 9

- Real Sociedad ta yi rashin nasara a hannun Barcelona a gida a wasan farko na daf da na kusa da karshe a gasar Copa del Rey da suka fafata a ranar Alhamis

- Barcelona ta ci kwallon ne tilo ta hannun Neymar Da Silva a bugun fenariti a minti na 21 da fara tamaula

Barcelona ta karya camfin shekaru 9
Barcelona ta karya camfin shekaru 9

Daya wasan da aka buga Atletico de Madrid ce ta doke SD Eiber da ci 3-0.

'Yan wasan da suka ci wa Atletico kwallayen sun hada da Antoine Griezmann da Angel Correa da kuma Kevin Gameiro.

SD Eiber da Atletico Madrid za su kara a wasa na biyu a ranar 25 ga watan Janairu, yayin da Barcelona za ta karbi bakuncin Real Sociedad a ranar 26 ga watan na Janairu.

A wani labarin kuma, Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Celta de Vigo da ci 2-1 a wasan daf da na kusa da karshe a gasar Copa del Rey da suka kara a Bernebeu a ranar Laraba.

Iago Aspas ne ya fara ci wa Celta kwallo a minti na 64, daga baya ne ne Madrid ta farke ta hannun Marcelo Vieira Da Silva.

Daga baya Celta ta kara cin kwallo ta biyu ta hannun Jonny.

A daya wasan na biyu kuwa Alcorcon ce ta yi rashin nasara a hannun Deportivo da ci biyu da babu ko daya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel