Abubuwa 7 da ya kamata ka sani akan Adama Barrow

Abubuwa 7 da ya kamata ka sani akan Adama Barrow

A ranan 1 ga watan Disamba, 2016, Adama Barrowa ya lashe zaben shugaab kasar Gambiya inda ya kayar da shugaba mai ci Yahaya Jammeh.

Abubuwa 7 da ya kamata ka sani akan Adama Barrow
Abubuwa 7 da ya kamata ka sani akan Adama Barrow

Ga abubuwa 7 da zaku iya sani game da Adama Barrow

1. Kabilarsa

Adama Barrow na alaka da kabilu masu yawa. Mahaifiyarshi yar kabulan fula ce yayinda mahaifinsa da kabilar Mandika ne.

2. Addini

Adama Barrow dan addinin musulunci ne kuma dan ahlus sunnah. Yana yawan ambaton sunan Allah a maganganunshi. Kana kuma yana halartan bukukuwan addini kuma yana alfaharin musulunci.

KU KARANTA: An rantsar da Adama Barrow

3. Kwallon kafa

Adama Barrow masoyin kwalon kafa ne. masoyi kungiyar kwallon kafan Arsenal ne.

4. Karatunsa

Adama Barrow ya halarci makarantan firamaren Koba Kunda primary school sannan ya karasa makarantan sakandaen Crab Island a Banjul kafin ya tafi makaranta Musulin High School. Bayan ya arasa karatun sakandare, yayi aiki kafin ya tafi Birtaniya karatun jami’a.

5. Rayuwan aurensa

Adama Barrow ya auri mata 2. Dukkansu yan kabilan Fula. Yanada yara 4 yanzu. Dan shi guda daya ya rasu sanadiyar cizon kare kwanakin baya.

6. Hijiransa

Yayi hijira zuwa kasar Ingila a shekarar 200 inda yayi aiki a matsayin mai gadi a Argos yayinda yake karatu a jami’a

7. Kasuwanci

Barrow shine shugaban kamfanin gidaje mai suna Majum Real Estate a kasar Gambiya

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel