Bamu gane yadda barayi suke guduwa daga Najeriya ba tare da fasfot ba - EFCC ga Immigration

Bamu gane yadda barayi suke guduwa daga Najeriya ba tare da fasfot ba - EFCC ga Immigration

- Hukumar EFCC ta rude akan yadda barayin gwamnati ke guuwa daga Najeriya bayan an kwace fasfot din ta

- EFCC tayi alkawarin cewa zatayi aiki da hukumar shoga da ficen Najeriya wajen hana barayi guduwa daga kasa

Bamu gane yadda barayi suke guduwa daga Najeriya ba tare da fasfot ba- EFCC ga Immigration
Bamu gane yadda barayi suke guduwa daga Najeriya ba tare da fasfot ba- EFCC ga Immigration

Hukumar hana almundahan da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta bayyana a ranan Laraba, 18 ga watan Junairu cewa ita bata gani yadda barayin gwamnati ke guduwa daga Najeriya ba tare da fasfot ba.

Shugaban hukumar na shiyar kudu masi kudu Ishaq Salilu,wanda ya bayyana wannan yayi kira hukumar shiga da ficen Najeriya da su hada karfi da karfe wajen tabbatar da cewa barayin gwamnati ba zasu daman guduwa.

KU KARANTA: Majalisa ta bukaci Buhari ya baiwa NJC kudinta

Jaridar Daily postta bada rahoton cewa Salihu ya fadi wannan ne lokacin da ya samu bakuncin kontrollan hukumar shiga da ficen Najeriya shiyar jihar Ribas, A. B. Yarima a ofishin sa.

Salihu yace: “ Muna addu’a akan hada kai mai zurfi. Muna jin dadin hada kai da ku.yadda barayin ke guduwa daga Najeriya na bamu mamaki.”

Shi kuma Yarima ya mayar da martani, yace: “ Muna shirya da cigaba da hada kai tsakanin hukumar shiga da fice da hukumar EFCC.”

A bangare guda, hukumar EFCC ta kwace jirgin tsohon gwamnan jihar Borno,da wasu yan siyasa 2.

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel