Buhari ya sa yan Najeriya sun shiga kangin bauta – Kungiyar matasan Arewa

Buhari ya sa yan Najeriya sun shiga kangin bauta – Kungiyar matasan Arewa

Shugaban kungiyar matasan Arewa, Alhaji Shettima ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da sanya yan Najeriya sama da miliyan 160 cikin kangin bauta.

Buhari ya sa yan Najeriya sun shiga kangin bauta – Kungiyar matasan Arewa
Shettima Yerima

Da yake magana tare da jaridar Sun, shugaban matasan arewan ya bayyana cewa yan arewa sun kware gurin kwatar mulki ne kawai amma basu amfani da shi gurin kawo cigaba a yankinsu.

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya na danasanin zaban Buhari – Makarfi

Yace: “Abun bakin ciki ne cewa Najeriya na fuskantan rikice-rikice da matsaloli da dama, duk da gwagwarmayanmu da sadaukarwa gurin yaki kan mulkin karya.

“Mun kasance muna yaki don mulkin demokradiya amma abun bakin ciki, masu zarrafi sun mamaye tsarin gwamnati. Yawanci su basu sadaukar da komai ba, kuma wannan ne yasa basu jin ko wani ciwo a kan yadda abubuwa ke tafiya a kasar.

“Wadanda suka sadaukar da kawunansu sun tashi a tutar babu, kuma shi yasa sama da yan Najeriya 160 ke cikin kangin bauta.

KU KARANTA KUMA: Tsagerun Adaka Boro Avengers sun saki sabon sako

“Mutane na sa ran cewa kokarin da yan Najeriya sukayi don ganin sun fito da wani sabon jam’iyya; don ganin cewa wani jam’iyyar adawa ta karbi mulki daga hannun jam’iyya mai ci shekaru da dama, zuwa yanzu ya kamata ace yan Najeriya sun fara dariya, suna ganin chanji da shakar numfashi mai dadi, amma hakan bai samu ba. Al’amarin ya dada tabarbarewa ne fiye da yadda muke zato.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel