To fa! Wata mata ta watsa wa saurayin ta asid

To fa! Wata mata ta watsa wa saurayin ta asid

-A wani lamari da ba kasafai ake samun aukuwar irinsa ba, wata matashiya 'yar shekara 26 ta watsawa wanda za ta aura asid a garin Bangalore da ke India.

-Lydia Yeshpaul ta bayyana a wata kotu da ke Bangalore ne bayan an tuhume ta da wannan laifi.

To fa! Wata mata ta watsa wa saurayin ta asid
To fa! Wata mata ta watsa wa saurayin ta asid

Ana zarginta da watsa asid din a fuskar Jayakumar Purushottan da kuma yunkurin kashe shi.

Mista Purushottam ya ce iyayensa ba su amince da aurensu da yarinyar ba a kan dalilai na addini.

Wani babban jami'in 'yan sanda ya shaida wa BBC cewa wannan ne karon farko da ofishin 'yan sanda na wannan yankin ya fuskanci irin wannan lamarin na a samu wata da watsawa wani acid.

A wani labarin kuma, An haifi wata jaririya a cikin motar 'yan sanda, bayan motar iyayenta ta lalace a kan hanyarsu ta zuwa asibiti a London.

Mai jegon, Emily McBride da abokin zamanta Thomas Carson na kan hanyarsu ta zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Royal Stoke lokacin da motarsu ta mutu.

'Yan sanda daga ofishin Staffordshire sun ɗauke su zuwa asibiti a bayan motarsu ta sintiri.

Sai dai, kafin Emily ta fita daga motar, sai ta haife jaririyarta wadda aka raɗawa suna Darcey.

Daga nan sai aka ƙarasa da mai jego da jaririyarta ɗakin karɓar haihuwa.

Mai jegon Ms McBride ta yaba wa 'yan sanda saboda kai ta asibiti a kan lokaci, a cewarta ba don 'yan sanda ba da ta haihu a cikin cunkoson motoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel