LABARI DA DUMI-DUMI: Osinbajo zai zama shugaban kasa

LABARI DA DUMI-DUMI: Osinbajo zai zama shugaban kasa

– Shugaba Buhari ya rubuta takarda ga Majalisa cewa zai tafi hutu

– Mataimakin sa, Osinbajo zai karbi ragamar Kasar

– Shugaba Buhari zai yi tafiya na kwanaki 10

LABARI DA DUMI-DUMI: Osinbajo zai zama shugaban kasa
LABARI DA DUMI-DUMI: Osinbajo zai zama shugaban kasa

Rahotanni da ke zuwa mana suna nuna cewa Shugaba Buhari zai tafi hutun kwanaki 10. shugaban majalisar dattawar Kasar Bukola Saraki ya karanto takardar shugaban kasar da ke neman izini.

Shugaba Buhari ya nemi Majalisa ta amince da Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin mukaddashin shugaban kasar. Wannan dai yana cikin kundin tsarin mulkin kasar sashe na 145 bangare na I.

KU KARANTA: Abin da ya hana Buhari zuwa Maiduguri

Kuma ba dai wannan bane karo na farko da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya tafi hutu, aka mika shugabancin kasar hannun Yemi Osinbajo ba. A watan Fabrairun bara da kuma Yunin shekarar yayi hakan. Shugaba Buhari ya bayyana a shafin sana Facebook cewa zai tafi hutu Kasar Ingila na kwanaki 10.

A jiya ne Abba Kyari ya isa Garin Maiduguri tare da sauran tawagar shugaban kasar da ya jagoranta domin jaje ga mutanen Borno. Sauran tawagar sun hada da Shugabannin Hafsun Sojojin Kasar da kuma Ministocin tsaro da na yada labarai.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel