Yan Najeriya na danasanin zaban Buhari – Makarfi

Yan Najeriya na danasanin zaban Buhari – Makarfi

Yan Najeriya na danasanin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma tunkude jam’iyyar Peoles Democratic Party (PDP), cewar Sanata Ahmed Makarfi, shugaban kwamitin riko.

Yan Najeriya na danasanin zaban Buhari – Makarfi

Shin yan Najeriya sun gaji da Buhari ne?

Mista Makarfi wanda yayi magana wani taron jam’iyya a jiya a Abuja, yace jam’iyyar ta PDP na kokarin sabonta tsari saboda 2019.

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta tura sojoji da jiragen yaki kasar Gambiya

Yace wasu yan Najeriya sun riga sun fara bada hakuri kan tunkudar da jam’iyyar, cewa amma dai suna da wani dama da kuma zaben PDP don ta dawo mulki a 2019.

“Muna sake duba da sake fasalin jam’iyyar, hukuncin Port Harcourt kawai muke jira kuma muna addu’an samun hukunci mai kyau da zai dawo da burin mutane.

“Ayi adalci ta yadda duniya gabaki daya zata ga cewan masu shari’a nayin abunda ya dace.

“Idan kuka kawar da yan adawa, babu wanda zai tsira. Don ci gaban Najeriya ne cewa babu adawa.

“Wasu mutane sun riga sun fara bada hakuri kan tunkude mu daga mulki, amma muna fada masu cewan su kuma zaben mu”.

KU KARANTA KUMA: Tsagerun Adaka Boro Avengers sun saki sabon sako

Ya shawarci yan uwansa yan Jam’iyya da su yi suka cikin hikima su kuma kawo mafita. Ya gargadi yan jam’iyya kan ci da ceto.

Source: Legit

Mailfire view pixel