Gwamna Kashim Shettima zai baiwa matasa 10,000 aikin yi

Gwamna Kashim Shettima zai baiwa matasa 10,000 aikin yi

Gwamnan jihar Borno daya sha fama da rikicin Boko Haram, Kashim Shettima ya kaddamar da wani sabon kamfanin sarrafa sinadarin da aka kashe makudan miliyoyin naira wajen gina shi.

Gwamna Kashim Shettima zai baiwa matasa 10,000 aikin yi
Gwamna Kashim Shettima

Gwamnan ya bayyana cewar gwamnatinsa ta gina kamfanin ne don ta sama ma dimbin matasan dake jihar ayyukan yi, tare da samar ma jihar kudaden shiga. Gwamnan ya bayyana haka ne yayin ziyarar aiki daya kai zuwa kamfanin a ranar Litinin.

KU KARANTA:Magidanci ya sha da kyar daga wani mummunan hadari daya rutsa da shi

Ga wasu daga cikin hotunan kamfanin nan:

Gwamna Kashim Shettima zai baiwa matasa 10,000 aikin yi

Gwamna Kashim Shettima zai baiwa matasa 10,000 aikin yi

Gwamna Kashim Shettima zai baiwa matasa 10,000 aikin yi

Gwamna Kashim Shettima zai baiwa matasa 10,000 aikin yi

Gwamna Kashim Shettima zai baiwa matasa 10,000 aikin yi

Gwamna Kashim Shettima zai baiwa matasa 10,000 aikin yi

A wani labarin kuma gwamna Kashim ya umarci kungiyoyin sa kai dasu tattara inasu inasu su fita daga jihar tunda a cewar gwamnan sun gaza tallafa ma mutanen da bala’in Boko Haram ya shafa. Gwamnan ya zargi kungiyoyin ne da rashin tabuka komai duk da irin da suke cewa suna kashewa, in banda albashin da suke biyan kawunan su.

Jaridar Premium Times ta ruwaito gwamnan yana fadin: “muna da jerin sunayen dukkanin kungiyoyin sa kai dake jihar nan. wasu kungiyoyin majalisar dinkin duniya suna iya bakin kokarinsu, amma fa bamu gamsu ba.”

Gwamnan yace zaka ji majalisar dinkin duniya tana fadin ta kashe miliyoyin daloli akan tallafa ma yan Boko Haram, amma sai kaga fiye da rabin kudaden nan sun kare a albashin ma’aikatansu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel