Najeriya ta tura sojoji da jiragen yaki kasar Gambiya

Najeriya ta tura sojoji da jiragen yaki kasar Gambiya

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta tura sojoji 200 zuwa Senegal domin karfafa rundunar kasashen Ecowas da ke shirin kawar da Shugaba Yahya Jammeh na Gambia da karfin tuwo.

Tuni rundunar sojin Senegal suka isa iyakar kasar ta Gambia domin tilasta wa Mista Jammeh ya sauka daga mulki.

Shugaba Jammeh ya ki sauka daga mulki duk da kayen da ya sha a hannun Adama Barrow a zaben watan Disamba.

Senegal ta bashi zuwa tsakar daren ranar Talata domin ya sauka, ko kuma ta afka masa.

KU KARANTA KUMA: Wadanda ke ihun ‘Allahu Akabar’ suna kashe mutane zasu shiga wuta – Sultan na Sokoto

Amma tuni ya ayyana dokar-ta-baci ta wata uku sannan majalisar dokoki ta tsawaita wa'adinsa na tsawon lokacin.

Yunkurin shawo kan rikicin ta hanyar diflomasiyya ya ci tura kawo yanzu.

Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar ta ce tawagar ta hada da dakaru da kuma jiragen yaki da kuma masu tattara bayanan sirri.

Rundunar za ta je Senegal ne domin jiran ko-ta-kwana game da tashin hankalin da ka iya barke wa saboda rikicin siysar da ake fama da shi a Gambia.

Kalli hotuna a kasa:

Nigeria ta tura sojoji da jiragen yaki kasar Gambiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel