Sarki ya sha da kyar bayan wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai mai hari

Sarki ya sha da kyar bayan wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai mai hari

A jiya ne wasu yan bindiga suka kai hari ga ayarin motocin sarkin Jema’a (Kafanchan) Alhaji Muhammad Isa Muhammad II a Samarau Kataf, karamar hukumar Zangon Kataf dake jihar Kaduna, inda suka lalata motoci uku.

Wasu yan bindiga suka kai hari ga ayarin motocin Sarki a Kudancin Kaduna

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kai wa sarkin hari ne a hanyarsa ta dawowa daga Kafanchan bayan ya halarci wani taron tsaro tare da gawamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufai, kan al’amuran da suka shafi kashe-kashen da akayi kwanan nan a Kudancin Kaduna.

Ciroman masarautar Jema’a, Alhaji Kabiru Tanko, wanda ya sha da kyar ya fada ma jaridar Daily Trust cewa an kai masu hari ne da misalign karfe 8:00 na dare a Samaru Kataf bayan sun halarci wani taro tare da gwamna.

KU KARANTA KUMA: Zahra Buhari tayi murnar cikarta wata daya da aure

Yace: “Lokacin da muka isa Samaru Kataf, wasu matasa dauke da makamai suka zagaye mu da makamai iri-iri kuma suka fara kai wa ayarinmu hari. A take muka juya zuwa Kachia don tsirar da kanmu”.

Ciroman ya yaba ma gwamnatin Gwamna El-Rufai da kuma gwamnatin tarayya kan dawo da hukumomin tsaro a Kudancin Kaduna.

Ya bukaci gwamnati da tayi kyakkyawan bincike a rikicin Kudancin Kaduna, ya kara da cewa a hukunta wadanda keda alhakin rikicin ba tare da fargaba ko alfarma ba.

Har ila yau yayi kira ga musulmai da Kiristoci a jihar da su rungumi zaman lafiya, kamar yadda ko wani addini ya koyar da zaman lafiya, domin ci gaban jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel