Rufe filin jirgin Abuja: Mabambantan ra'ayoyi na ci gaba da kwaranya

Rufe filin jirgin Abuja: Mabambantan ra'ayoyi na ci gaba da kwaranya

- Korafe-korafen da Majalisar Dattawa ta samu akan batun rufe filin saukar jiragen sama na Abuja saboda a yi masa gyara ya sa majalisar tayi wani dogon zama domin ta saurari jama'a da damuwarsu.

- Majalisar ta saurari kwararru akan harkokin jiragen sama da masu ruwa da tsaki a lamarin, musamman a harkokin sufurin sama.

Rufe filin jirgin Abuja: Mabambantan ra'ayoyi na ci gaba da kwaranya
Rufe filin jirgin Abuja: Mabambantan ra'ayoyi na ci gaba da kwaranya

Sanata Joshua Lidani da yayi magana akan matsayinsu bayan sun samu bayanai yace a ganin majalisar bai kamata a rufe filin ba. Idan akwai gyara ya kamata a yi aikin amma jirage na sauka.

Saidai masana sun ce hakan ba zai yiwu ba saboda za'a dauki tsawon lokaci ana aikin tare da kutuntawa mutane.

KU KARANTA KUMA: Jama’a sun aika da wani dan fashi Lahira a Bayelsa

Majalisar ta ce su koma su yi anfani da abubuwan da aka fada su dauki matsayi ba sai sun koma wurin majalisar ba.

Shi ma dan majalisar wakilai Injiniya Aliyu Muhammad yace akwai kwararan dalilai da suka sa gwamnati ta dauki matakin rufe filin. Yace yawancin gwamnatoci basa kula da yin gyara. Yace duk duniya babu inda ake barin filin jirgin sama yayi shekaru talatin babu gyara. Dole ce ta sa sai an rufe domin rashin gyara da ba'a yi ba na tsawon lokaci, inji Injiniya Muhammad.

Bayan ya kwashi sa'o'i hudu yana amsa tambayoyi daga majalisar, karamin ministan sufuri mai kula da harkokin jiragen sama Sanata Hadi Sirika ya jaddada sanarwar da gwamnatin tarayya tayi na cewa za'a rufe tashar daga ranar 8 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel