Rundunar sojin Najeriya sun fasa kasar Gambiya domin tunbuke Jammeh

Rundunar sojin Najeriya sun fasa kasar Gambiya domin tunbuke Jammeh

- Rundunar sojin ruwa, na sama, da na kasa zasu hada kai da rundunar ECOWAS akan batakashin wajabtawa Yahaya Jammeh ya sauka kan karagar mulki a Gambiya

- Wata jirgin ruwan yakin Najeriya NNS tana hanya yanzu zuwa kasar Ghana bayan ta bar Legas.

- Shugaba Yahaya Jammeh ya sa dokar ta baci a kasar Gambiya na tsawon kwanaki 90

Rundunar sojin Najeriya sun fasa kasar Gambiya
Rundunar sojin Najeriya sun fasa kasar Gambiya

Kungiyar ECOWAS ta baiwa shugaban kasar Gambiya Yahaya Jammeh wa’adin ranan Alhamis 19 ga watan Junairu ya sauka ko kuma a cire shi da karfin soja.

Gwamnatin tarayyar Najeriya zata aika sojinta su hadu sojin ECOWAS a kasar Senegal kafin ranan Alhamis da wa’adin da aka ba Yahaya Jammeh zai kare.

KU KARANTA: Majalisa zata bincike kudin makarantan Chibok

Jaridar Punch ta baa rahoton cewa wata majiya a hukumar sojin sama ta bada rahoton cewa rundunar sojin sama, da na ruwa da kuma na kasa zasu taimaka da mazaje wajen yakin.

Majiyar tace shugaban rundunar sojin sama, Iya mashal Sadique Abubakar,ya tattauna da sojin da safiyar laraba,18 ga watan Junairu kafin su tafi kasar Senegal.

Yace: “Zan iya tabbatar muku da cewa mazajen rundunar sojin sama zasu tafi kasar Senegal gobe laraba. Shugaban rundunar sojin sama Sadique Abubakar,zaiyi musu Magana a Kainji base a jihar Neja.

“Shugabannin hukumonin tsaro jihohin ECOWAS sun hadu a Abuja ranan asabar inda suka tattauna yawan mazajen da kowani kasa zata bayar domin tunbuke Yahaya Jammeh da karfi da yaji. Mazajen zasu tsaya tsawon mako 2 a kasar Senegal."

Asali: Legit.ng

Online view pixel