‘Ba nayi a dawo min sadaki na’ – Inji wani Ango

‘Ba nayi a dawo min sadaki na’ – Inji wani Ango

Wani ma’abocin kafar sadarwa ta Facebook Isaiah Otong ya koka kan yadda Amaryarsa ta rabu da shi bayan ya kashe kudi wuri na gugan wuri har N950,000 a bikin ta, daga bisani yanzu Otong ya bukaci a dawo masa da kudadensa, ya fasa auren.

‘Ba nayi a dawo min sadaki na’ – Inji wani Ango
Ango da amarya yayin bikin

Otong asalin jihar Akwa Ibom ya nuna bacin ran nasa ne bayan amaryarsa ta gudu sati biyu da yin bikin aurensu.

Isaiah Otong yace: “Ina bayyana kuka na ne saboda bana son wani ya fada tarkon wannan matar tawa don kada Clestus ta yaudare shi. Jama’a ku bi a hankali da iyalan gidan Idongesit John Udoma yan garin Ikot Anyiefon daga kauyen Ikot Okim na karamar hukumar Abot Akara. Ga lissafin abubuwan dana kashe wajen neman auren ta.''

KU KARANTA:An fara tantance ma’aikatan lafiya a jihar Nassarawa

“Kunga dai da fari na siya yadi goma na leshi, singlet guda shida, bantai 3, atamfa guda 5, takalma 2 da safa, sandan tafiya, agogo 7, tawul, kwalban giya 19, lemun kwali kwali 2, lemun kwalba 25, katan din giya 62, doya kwara 11, bunsuru 2, kaji 6, kudin abinci 300,000, masu kida 150,000, kudin sadaki 600,000.” Inji Ango.

‘Ba nayi a dawo min sadaki na’ – Inji wani Ango

Angon ya karkare da cewa, “sai dai duk da wadannan makudan kudade dana kashe sai amaryar tawa ta gudu gidansu a ranar 18 ga watan Oktoba na 2016. Jama’a ku fada min idan ba yaudara aka shirya ba menene wannan?''

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel