Janar Buratai yayi magana game da Boko Haram

Janar Buratai yayi magana game da Boko Haram

– Shugaban Hafsun Sojin Kasar Najeriya Janar Buratai yayi magana game da Yaki da Boko Haram

– Buratai yace ‘Yan ta’addan Boko Haram sun ba su tsoro

– Janar Tukur Buratai yayi magana game da gonakin macizan sa

Janar Buratai yayi magana game da Boko Haram

Janar Buratai yayi magana game da Boko Haram

Shugaban Hafsun Sojin Najeriya, Lafatana Janar Tukur Yusuf Buratai yayi magana game da Yakin Boko Haram a wata hira da yayi kwanaki da Jaridar Daily Trust. Janar Buratai yace akwai lokacin da Mayakan Boko Haram suka ba su tsoro.

Janar Buratai yace akwai lokacin da ‘Yan Boko Haram suka harbo wani makami ga Rundunar Sojin Kasar. Sai dai an yi dace Sojojin sun nuna bajinta wajen tare harin Tun daga nan ne ‘Yan Boko Haram suke tsere daga Dajin na Sambisa inji Janar din.

KU KARANTA: Boko Haram: Shugaba Buhari ya mika ta'aziyya

Buratai ya kuma bayyana dalilin da ya sa yake kiwon macizai a gonar sa. Janar din yace ya saba aran-gama da macizai a rayuwar sa a wurare dabam, ko dama dai can macizan suna ba sa sha’awa. Hakan dai ta sa ya fara kama su yana kiwo.

A jiya ne Rundunar Sojin Najeriya da wasu Manyan Ministoci suka zagaya da ‘Yan Kungiyar nan ta BBOG watau BringBackOurGirls zuwa Dajin Sambisa domin gani da idon su. Sai dai da suka wuce kusan awa biyu suna yawo a sararin samaniya. Madam Oby Ezekwensili tace ba shakka Dajin na da mugun girma.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel