Birtaniya za ta fice daga tarayyar kasashen Turai gaba daya

Birtaniya za ta fice daga tarayyar kasashen Turai gaba daya

- Firai ministar Birtaniya, Theresa May, ta sanya wasu batutuwa guda 12 da ta ce su ne mafi mahimmanci ga fitar kasar tata daga Tarayyar Turai

- Misis May ta kuma kara da cewa tana son Birtaniya ta fice daga tarayyar dungurungum ba wai rabi da rabi ba

Birtaniya za ta fice daga tarayyar kasashen Turai gaba daya
Birtaniya za ta fice daga tarayyar kasashen Turai gaba daya

Nan gaba kadan ne dai a ranar Talatar nan ake sa ran Firai ministar za ta yi wani jawabi ga 'yan kasar kan jadawalin da ta fitar wajen ficewa daga Tarayyar Turai.

Ana dai sa ran Birtaniya za ta fara shirin ficewa daga Tarayyar ta Turai ne, kafin karshen watan Maris.

A wani labarin kuma, An haifi wata jaririya a cikin motar 'yan sanda, bayan motar iyayenta ta lalace a kan hanyarsu ta zuwa asibiti a London.

Mai jegon, Emily McBride da abokin zamanta Thomas Carson na kan hanyarsu ta zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Royal Stoke lokacin da motarsu ta mutu.

'Yan sanda daga ofishin Staffordshire sun ɗauke su zuwa asibiti a bayan motarsu ta sintiri.

Sai dai, kafin Emily ta fita daga motar, sai ta haife jaririyarta wadda aka raɗawa suna Darcey.

Daga nan sai aka ƙarasa da mai jego da jaririyarta ɗakin karɓar haihuwa.

Mai jegon Ms McBride ta yaba wa 'yan sanda saboda kai ta asibiti a kan lokaci, a cewarta ba don 'yan sanda ba da ta haihu a cikin cunkoson motoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel