Abu 5 da Shekau ya fada a sabon faifan da ya fitar game da harin jami'ar Maiduguri

Abu 5 da Shekau ya fada a sabon faifan da ya fitar game da harin jami'ar Maiduguri

Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram wanda kuma ya bada sanarwar daukan alhakin kai harin Masallacin Jami'ar Maiduguri.

Abu 5 da Shekau ya fada a sabon faifan da ya fitar game da harin jami'ar Maiduguri
Abu 5 da Shekau ya fada a sabon faifan da ya fitar game da harin jami'ar Maiduguri

A wani faifan da ya fitar ba tare da hotonsa ba, Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram ya dauki alhakin kai hari cikin masallacin Jami'ar Maiduguri tare da shan alwashin kara kai har-hare har sai an tuba ana musulunci irin nasu.

1. Ya fara da jan ayoyin alqur'ani mai girma:

A jawabinsa dai ya fara ne da jan aya daga Kur'ani Mai Tsarki inda Abubakar Shekau din yace bam din da ya tashi jiya Litinin da safe 'yanuwansu ne suka tayar da fatan Allah ya karbi ran 'yan kunar bakin waken.

2. Yace ana kafirci a cikin masallacin:

A cikin faifan har ila yau dai Shekau din yace wai masallacin da aka tada bam din ba masallaci ba ne domin ana kafirci ciki ana hada masallaci da dimokradiya. Yace abun da ake yi cin amanar Annabi ne.

Abu 5 da Shekau ya fada a sabon faifan da ya fitar game da harin jami'ar Maiduguri
Abu 5 da Shekau ya fada a sabon faifan da ya fitar game da harin jami'ar Maiduguri

3. Yace wai za su ci gaba da kai hare-haren:

Inji shugaban na kungiyar Boko Haram din, Abubakar Shekau yace zasu kara ci gaba da kai irin hare-haren har sai an je lahira a tsaya gaban Allah a yi shari'a.

4. Ya sake kiran mutane da su bi irin kalar akidar su:

Kamar dai a cikin faya-fayan da ya ke fitar wa a kwanan baya, a cikin wannan faifan ma Shekau ya kira duk wanda yake son yayi muslunci da gaske, to acewar sa ya zama wajibi ya tuba ya bi akidarsu saboda su ne suke aikin Allah, suke yin addinin Allah tsantsa.

Abu 5 da Shekau ya fada a sabon faifan da ya fitar game da harin jami'ar Maiduguri
Abu 5 da Shekau ya fada a sabon faifan da ya fitar game da harin jami'ar Maiduguri

5. Ya kuma yi tsokaci kan dajin Sambisa:

Game da dajin Sambisa kuma, shugaban na kungiyar ta'addacin na Boko Haram Abubakar Shekau ya sake nanatawa cewa babu abun da ya samesu suna nan daram duk karya ake yiwa 'yan Najeriya.

Ya bada hujjar yin anfani da mata wajen kai hare-haren kunar bakin wake wanda ya hada da na baya bayan nan a Jami'ar Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel