An tashi wasa canjaras tsakanin Man United da Liverpool

An tashi wasa canjaras tsakanin Man United da Liverpool

Anyi gumurzu sosai a filin wasa na Old Trafford gidan Manchester United yayin da wasa ya tashi ca daya da daya tsakanin Man Utd da Liverpool.

An tashi wasa canjaras tsakanin Man United da Liverpool

Dan wasan Liverpool James Milner ne ya fara saka kwallo a ragar Man Utd a bugu daga kai sai gola, bayan shahararren dan wasan Man Utd Pogba ya kama kwallo da hannu a cikin harabar gola.

Haka dia aka cigaba da kai ruwa rana, akayi gwarzo akayi mari, amma wasa ya ki Liverpool sakamakon sune suka fi buga wasan, kuma suka danna Man Utd, amma kwallo yaki shiga.

KU KARANTA:Sevilla ta karya alkarin Real Madrid

Abinka da wasa, sai a bayan an dawo hutun rabin lokaci ne yan wasan Mancester suka bude wuta, suka dinga aza ma Liverpool azaba, inda Wayne Rooney, Pogba da Mkhitaryan suka kusan farke wasa a mintuna na 60 na 70.

Sai a minti na 87 ne dna wasan nan Zlatan Ibrahimovic ya sanya mata kwallo kai, da haka wasa ya koma canjaras. Da wannan a yanzu Man Utd tana nan a matsayinta na 6 yayin da Liverpool ke matsayi na 3.

A wani labarin kuma Man Utd zata je bakonta gidan kungiyar Stoke City a gida a ranar 21 ga watan Janairu.

Ku biyo mu https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel