Bamu kama wani mutum farar fata a dajin Sambisa ba – Buratai

Bamu kama wani mutum farar fata a dajin Sambisa ba – Buratai

Babban hafsan mayakn sojan kasa Laftanar Janar Tukur Buratai yace dakarun soji sun tabbatar da cewar sun kashe wani mutum farar fata a yayin barin wutar daya biyo bayan yunkurin sojoji wajen kwace dajin Sambisa.

Bamu kama wani mutum farar fata a dajin Sambisa ba – Buratai
Bamu kama wani mutum farar fata a dajin Sambisa ba – Buratai

Cikin wata hira da Buratai yayi da jaridar Daily Trust yace lamarin ya faru yayin da dakarun soji suka kaddamar da wani hari ne a dajin Sambisa.

“Bamu kama wani mutum farar fata ba, amma yayin da dakarun mu ke musayar wuta da yayan kungiyar Boko Haram, sun kashe wani farar fata daga cikin yan ta’addan, wata kila ganin wannan ne ya sanya aka zaton ko mun kama wani farin fata,” inji Buratai

KU KARANTA:Mutane 9 sun mutu yayinda Fulani makiyaya suka kuma kai hari jihar Niger

Buratai ya kara da cewa, hoton da ake watsa da sunan farar fatar da muka kama a dajin Sambisa ba gaskiya bane, wannan wani bature ne da sojojin kasar Kamaru suka taba kwato shi bayan yan Boko Haram sun sace shi. Amma dai tabbasa wani mutum farar fata ya fafata da jami’an mu, amma mun kashe shi.

“Wannan shine tabbataccen labari da na ke da shi,” inji Buratai.

A wani labarin kuma, dakarun sojin Najeriya sun shirya tsaf don zuwa kasar Gambiya don tabbatar da sun kifar da gwamnatin Yahaya Jammeh idna har bai sauka daga karagar Mulki ba zuwa ranar 19 ga watan Janairu.

Wani takarda a hukumance daga rundunar mayakan sojan kasa ta nuna an girke sama da dakaru 800 da za’a tura kasar ta Gambiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel