Hukumar Soji ta saki yan Boko Haram 257

Hukumar Soji ta saki yan Boko Haram 257

- Hukumar Sojin Nejriya ta saki yan Boko Haram 257 wadanda gwamnatin jihar Borno ta rike

- Sojin sunce wadanda aka saki basu da alaka da Boko Haram bayan an gudanar da bincike

Hukumar Soji ta saki yan Boko Haram 257
Hukumar Soji ta saki yan Boko Haram 257

Akalla wadanda aka zargi da alaka da Boko Haram 257 sun samu yanci. Hukumar sojin ta bayyana hakan ne a taron zagoyowar bikin soji a ranan Lahadim15 ga watan Junairu, a Maidiguri, Jaridar Punch ta bada rahoto.

Yayinda suke karban wadanda sojin suka ceto a hannun kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Leo Orabor lokacin taron.

Game da cewar Manjo Janar Irabor, wadanda aka saki basu alaka da Boko Haram bayan an gudanar da bincike sosai.

KU KARANTA: Abubuwan da suka faru karshen mako

''An binciki mutane 257 kuma an gano cewa masu gaskiya ne. taron murnan zaga yowar soji ne ya basu daman sakinsu albarkacin bikin.”

A bangaranshi, gwamna Shettima, wanda mataimakinsa ya wakilta, Mamman Durkwa, ya halarci taron kuma ya girmama sojin da suka rasa rayukansu, yace sun sadaukar da rayuwansu saboda hadin kan kasa.

A bangare guda, shugaban rundunar soji kasa, Laftanan Janar Tukur Buratai ya bayyana cewa shugaban Boko Haram Abubakar Shekau,ya koma wani wuri bayan rundunar soji sun kai wata hari dajin Sambisa.

Game da cewar Buratai, Shekau yaji ruwan wuta sai ya gudu wani wuri, kuma soji na biye da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel