Rundunar soji sun gano gawawwakin yan ta’addan Boko Haram a kabari

Rundunar soji sun gano gawawwakin yan ta’addan Boko Haram a kabari

Rundunar sojin Najeriya sun gano wani makabarta da yan ta’addan Boko Haram ke amfani dashi gurin binne wasu daga cikin yan mambobin su.

A cewar Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman a wata sanarwa a ranar Lahadi, 15 ga watan Janairu yace rundunar sojin Oeration Lafiya Dole ne suka gano kaburburan.

Rundunar soji sun gano gawawwakin yan ta’addan Boko Haram a kabari
Rundunar soji sun gano gawawwakin yan ta’addan Boko Haram a kabari

KU KARANTA KUMA: LABARI DA DUMI-DUMI: Bam ya tashi a masallacin jami’ar Maiduguri

Yace har ila yau rundunan sun kuma samo bama-bamai da alburusai nay an ta’addan.

Karanta sanarwan a kasa:

Rundunar soji sun gano gawawwakin yan ta’addan Boko Haram a kabari
Kabari mai zurfi da ake amfani dashi gurin binne yan ta'addan Boko Haram

“Rundunar bataliya 119 na Operation LAFIYA DOLE yayin sintiri a yau, sun ci karo da kaburburan yan ta’addan Boko Haram da suka tsere da raununkan bindiga suka kuma mutu bayan wani arangarama a ranar 13 ga watan Janairu 2017 sannan kuma aka binne su a cikin kaburbura masu zurfi.

Rundunar soji sun gano gawawwakin yan ta’addan Boko Haram a kabari
Bam da yan ta'addan ke amfani dashi

“Haka kuma rundunar sun samo wani gurnetin hannu 36 da kuma harsashi 12.7 X 108mm na yan ta’addan.

KU KARANTA KUMA: Abu mai taba zuciya: Kalli kyakyawan jaririn da aka yasar a makabarta

Rundunar soji sun gano gawawwakin yan ta’addan Boko Haram a kabari
Rundunar soji sun gano gawawwakin yan ta’addan Boko Haram a kabari

“Rundunan sun ci gaba da sintirinsu ta hanyar mamaye dukkan yankin Baga, Kangarwa da Dogonchikun tare da kudirin kama yan ta’addan Boko Haram da suka tsere.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel