Cikakken jadawalin jerin wasannin rukuni don neman shiga gasar AFCON na 2019

Cikakken jadawalin jerin wasannin rukuni don neman shiga gasar AFCON na 2019

An sake hada kasar Najeriya da ta Afirka ta kudu a wasan neman samun gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) da za’a fafata a shekarar 2019 wanda kasar Kamaru zata dauki nauyinsa.

Cikakken jadawalin jerin wasannin rukuni don neman shiga gasar AFCON na 2019
Kofin AFCON

An gwama kasashen Afrika ta kudu, Libya, Seyechelles da Najeriya a rukunin E, yayin da ita kuma kasar dake rike da kambun Kwatdebuwa zata kara da kasashen Guinea, Rwanda da kasar Afirka ta tsakiya. Duk kasar data samu damar darewa saman rukuninta zata samu gurbin a gasar ta AFCON.

KU KARNTA: Tambaya: Tsakanin shugaba Buhari da Jonathan, wa yafi iya kwalliya da khaki?

Cikakken jadawalin jerin wasannin rukuni don neman shiga gasar AFCON na 2019
Cikakken jadawalin jerin wasannin rukuni don neman shiga gasar AFCON na 2019

Idan za’a iya tunawa, kasar Afirka ta kudu ce ta kawo ma Najeriya tasgaron shiga gasar AFCON na bana, bayan ta lallasa Najeriya a gidanta, inda kuma aka yi canjarasa 2 da 2 a yayin da suka biyo mu gida. Da haka ne Najeriya ta rasa damar shiga, hakan ya baiwa kasar Afirka ta kudu da Congo daman shiga gasar da za’a fara a gobe Asabar 14 ga watan Janairu.

A wani labarin kuma Najeriya na kan gaba a rukunin B na neman shiga gasar kofin Duniya na 2018 da zai gudana a kasar Rasha.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel