A karo na biyu, Buhari ya aika da sunayen jakadu ga majalisa don tantancewa

A karo na biyu, Buhari ya aika da sunayen jakadu ga majalisa don tantancewa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar da garambawul ga jerin sunayen wadanda yake da muradin nadawa jakadun kasar nan bayan majalisar dattawa tayi watsi da sunayen a baya.

A karo na biyu, Buhari ya aika sunayen jakadu ga majalisa don tantancewa

Shugaban ya sake aika ma majalisar kwaskwararren jerin sunayen ne a ranar Alhamis 12 ga watan Janairu. Shugaban majalisar Abubakar Bukola Saraki ne ya karanto wasikar shugaban kasar.

Idan ba’a manta ba, a karon farko da shugaban ya aiko da sunayen, majalisar tayi watsi dasu a watan Nuwamba, inda suka ce akwai korafe korafe da dama game da sunayen da shugaban ya aiko. Bugu da kari tsohuwar matamakiyar gwamnan jihar Jos Pauline Tallen da Usman Bugaje daga Katsina sun ki amsan mukamin jakadan.

KU KARANTA: Talauci ya sanya wani mutum siyar da ‘ƙodarsa’ don biya ma ɗansa kudin makaranta

Sai dai an cire sunayen wasu mutane daga cikin kwaskwararren jerin sunayen da shugaba Buhari ya aika; cikinsu akwai kanin Sarkin Ife Adegboyega Ogunwusi, tsohon alkalin kotun koli George Oguntade, tsohon sanata Olorunnibe Mamora da tsohon mataimakin gwamnan jihar Neja Musa Ibeto.

Ga cikakken jerin sunayen nan:

Godwin Umoh (Akwa Ibom);

Christopher Okeke (Anambra);

Yusuf Maitama (Bauchi);

Baba Maigudu (Bauchi);

Stanley Douye (Bayelsa);

Stephen Uba (Benue);

Baba Ahmed Gida (Borno);

Utobong Asuquo (Cross River);

Frank Ofegina (Delta);

Joda Udoh (Ebonyi);

A karo na biyu, Buhari ya aika da sunayen jakadu ga majalisa don tantancewa

Yagwe Ede (Edo);

Eniola Ajayi (Ekiti);

Chris Eze (Enugu);

Sulieman Hassan (Gombe);

Sylvanus Usofo (Imo);

Aminu Dalhatu (Jigawa);

Ahmed Bamilli (Kaduna);

Deborah Yahaya (Kaduna);

D. Abdulkadir (Kano);

Haruna Arungungu (Kano);

Musa Udo (Katsina),

A karo na biyu, Buhari ya aika da sunayen jakadu ga majalisa don tantancewa

Mohammed Rimi (Katsina);

Tijani Bande (Kebbi);

Y. Aliu (Kogi);

Nurudeen Mohammed (Kwara),

Mohammed Isa (Kwara);

Adesola Omotade (Lagos);

Modupe Remi (Lagos);

Musa Mohammed (Nasarawa);

Ahmed Ibeto; (Niger);

Susan Aderonke Folarin (Ogun);

Jacob Daudu (Ondo);

Afolayon Adeyemi (Osun);

A. Olaniyi (Oyo);

James Dmika (Plateau);

Haruna Abdullahi (Plateau);

Orji Ngofa (Rivers);

A karo na biyu, Buhari ya aika da sunayen jakadu ga majalisa don tantancewa

Sahibi Isa Dada (Sokoto);

Kabir Umar (Sokoto);

Jika Ado (Taraba);

Goni Zana (Yobe);

Garba T. (Zamfara);

Bala Mohammad (Zamfara); and

Ibrahim Dada (FCT).

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel