Rundunar soji ta gano gawawwaki 15 na sojojin da su ka bace a filin daga

Rundunar soji ta gano gawawwaki 15 na sojojin da su ka bace a filin daga

- An gano gawawwakin Sojojin 15 da suka bace a yayin da su ke gwabza fada da mayakan Boko Haram

- An binne gawarwakin a Makabartar soji ta Maimalari

Rundunar soji ta gano gawawwaki 15 na sojojin da su ka bace a filin daga
Rundunar soji ta gano gawawwaki 15 na sojojin da su ka bace a filin daga

An gano gawawwakin sojojin wadanda da fari a ka sanar da batarsu a lokacin da suke fatattakar mayakan Boko Haram daga yankin Gashigar a jihar Borno a ranar 16 ga watan Oktobar shekarar 2015

Babban kwamandan yakin da aka yiwa lakabi da 'Lafiya Dole' Manjo Janar Lucky Irabor, ne ya bayyana haka a nazarin yakin da a ka yi wa lakabi da 'Operation Rescue Final' a sansanin soja na Maimalari, Maiduguri a ranar Laraba 11 ga watan Janairu.

Irabor ya ce, " An gano gawarwakin ne a wajen yankin tafkin Komadugu a Maiduguri, " a cikin gawarwakin da a ka gano akwai na Laftanar Kanar K. Yusuf, wani tsohon kwamandan bataliya ta 223".

Sannan ya kuma ce: "Tun lokacin a ka binne su a Makabartar sansanin soja na Maimalari da girmamawa irin ta soja."

Haka nan kuma, mayakan Boko Haram sun kashe sojoji guda 2 a ranar Talata 10 ga watan Janairu.

Irabor ya tabbatar da mutuwar gwarazan sojojin yayin wani taron manema labarai a Maiduguri babban birnin jihar orno.

A cewar Irabor, harin ya faru ne da yammacin Talata a wani yanki da a ke kira Mate a jihar Borno.

Amma bai bada sunayen sojojin da su ka mutu a fadan ba.

Ya ce sojoji sun kashe da dama daga 'yan ta'addan amma abin bakin ciki sojojin sun rasa rayukansu.

Ku biyomu a shafin mu na Facebook a https://www.facebook.com/naijcomhausa/ da Tuwita a https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel