Hanyoyi 6 da za ka gane dan Boko Haram a inda ka ke

Hanyoyi 6 da za ka gane dan Boko Haram a inda ka ke

-A ‘yan kwanakin nan jami'an tsaro na farin kaya DSS, suna ta cafke mayakan Boko Haram a wurare daban-daban kamar a Jihar Lagos da kuma sauran wurare a yankin kudu maso yammancin kasar nan

-Duba da wannan yasa aka bayar da wasu hanyoyi guda 6 da za ka iya gane dan Boko Haram a unguwarku domin a kiyaye

Hanyoyi 6 da za ka gane dan Boko Haram a inda ka ke
Hanyoyi 6 da za ka gane dan Boko Haram a inda ka ke

‘Yan Najeriya ya kamata su zama masu sanya idanu fiye da kowanne lokaci a baya. Ga wasu dabaru da zasu taimaka wajen gane dan Boko Haram a inda kuke:

1. Sayayya: Abu ne mai yiwu wa cewa yayin da "yan Boko Haram suka tsere za su tafi tare da miyagun akida da dabarar hada bama-bamai a duk inda suka je. Yayin da sojojin Najeriya suka bada bayani kan yanda za'a gane "yan Boko Haram sunce:

"Sanda duk ku ka ga mutum ya zo sayan kusoshi masu tarin yawan da shi kadai ba zai iya saya ba, ko kuma kun san shi sosai cewa shi ba magini ba ne a, toh akwai matsala."

Domin suna amfani da kusoshi wajen hada abubuwan farfashewa. Ya kamata ku sanar da "yan sanda.

2. Yanayin sanya tufafin jikinsu: Sun fi sanya dogayen kaya, amma kuma suna sanya rawani a kansu. Wannan kamar wani abu ne da kowa zai iya sawa sai dai kasancewar wadannan mutane guduwa suka yi za'a ga kayan su mafi yawancin lokaci sun fita hayyacin su, sannan sun yi dauda.

3. Yanayin jikin su: Za'a ga mafi yawanci ba sa aske gemu. Toh, idan kaga wani mutum a yankin ka da dogon gemu wanda kuma yayi datti, ya kamata ka yi taka tsan-tsan.

Duk da cewa abu ne mai wuya ace ga kalar fatar jikin su, idan kaga rukunin wasu mutane ramammu a yankin ka kuma baka sansu ba, ya kamata ka kiyaye

4. Yadda suke Sallah: Idan kai Musulmi ne ka san cewa, mafi yawancin Musulmai sai sun yi alwala sannan suke sallah. Su kuwa "yan Boko Haram ba sa alwala. Da ka haka, ka kiyaye ko a masallaci ka ga mutum yana sallah ba tare da alwala ba ka sanar da "yan sanda.

5. Zanen Jiki: Duk da cewa, wannan wata alama ce mai wuyar ganewa, har a yau bincike ya nuna cewa, mafi yawancin su suna da zanen ko alamar Boko Haram a wuyan su ko kuma dunduniyar su.

6. Zirga-zirga da ta ke abin zargi: Yana da matukar mahimmanci ku kiyaye da bakin dabi'u da kuma bakin al-amura da ke faruwa a yankinku sannan idan ba ku amince da su ba, sai ku gaggauta kai rahoto ga jami'an tsaro.

Ku biyo mu a shafin Facebook a https://www.facebook.com/naijcomhausa/ da kuma Tuwita a https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel