Budurwa tayi watsi da addinin Kirista, ta musulunta

Budurwa tayi watsi da addinin Kirista, ta musulunta

- Habiba Ishaku tayi watsi da addinin Kirista, kuma zata auri musulmi

- Yarinyar na da shekara 18

Budurwa tayi watsi da addinin Kirista, ta musulunta
Budurwa tayi watsi da addinin Kirista, ta musulunta

Habiba Ishaku, yar shekara 18 ta bar gida domin ta auri wani matashi Jamilu Lawal saboda iyayenta na son hanata.

Ta bar addinin Kirista zuwa addinin Islama a karamar hukumar Kankara a jihar Katsinan dikko.

A yayin zaman kotu a ranan asabar,11 ga watan Junairu,Habiba tace babu ruwanta da wani kara da wasu amintattun Stefanos Foundation da cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) sukayi a madadinta akan musuluntarta musulunci.

KU KARANTA: ECOWAS ta fasa zuwa kasar Gambia

Habiba ta mika wasika ga babban kotun jihar Katsina cewa ita fa shekarunta 18. Amma mahaifinta Mr Ishaku Tanko da wakilan coci suna cewa shekarunta basu kai hakan ba.

Lauyan cocin Mr Bawa Yakubu, yayi kira ga kotun tayi watsi da wasikar saboda da yaren hausa ta rubuta saboda haka kada ayi amfani da shi.

Lauyan Habiba, Mr Abu Umar, ya musanta hakan cewa tunda ana iya fassara wasikar zuwa harshen turanci,zata iya zama hujja a gaban kotu.

Yace: “Ko da sunce karamar yarinya ce, babu dokan da ya hana karamar yarinya fadn ran ta game da kundin tsarin mulkin Najeriya.

''Kana kuma Habiba ta fada ma kotun cewa hekarunta 18 ne ba 14 game yadda suke fada.”

Alkalin kotun, Justice Baraka Iliyasu-Wali,tayi kira ga Habiba ta zo kotu ranan 25 ga watan Junairu saboda da tabbatar da cewa itace ta rubuta wasikar.

https://www.facebook.com/naijcomhausa

https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel