Gobara tayi mummunar banna a Potiskum

Gobara tayi mummunar banna a Potiskum

- Gobara ta kona shaguna jama'a fiye da 50 a kasuwar Potiskum da ke jihar Yobe a Najeriya

- Wata gobara da ta tashi a kasuwar garin Potiskum da ke jihar Yobe a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ta kona akalla shaguna 50 na jama’a.

Gobara tayi mummunar banna a Potiskum
Gobara tayi mummunar banna a Potiskum
Asali: Facebook

Gobarar wadda ta shi da misalin karfe 1 na daren daya gabata, ta fi yin illa a bangaren masu hada-hadar kayan gwanjo da teloli da kuma bangaren da ake siyar da kwanuka.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, Alhaji Isa Sakatare ya shaida wa majiyar mu cewa, sun kafa kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike don kiyasta girmar dukiyar da aka yi asarar ta a gobarar.

Shugaban dai ya tabbatar cewa, gobarar ta haifar da gagarumar asarar da ba zai iya kiyasta ta ba har sai kwamitin ya fitar da sakamakon bincikensa.

A wani labarin kuma, Ana ci gaba da fuskantar karancin man kalanzir da kuma iskar gas a jihojin Najeriya, in da a halin yanzu ake siyar da lita guda ta kalanzir a kan Naira 300 ko fiye da haka, yayin da farashin iskar gas shi ma ya tashi sama. Rahotanni daga sassan kasar dai sun tabbatar da yadda matsalar ta jefa jama'a cikin mawuyacin hali.

Ku biyo mu a Facebook: https://web.facebook.com/naijcomhausa/

Ku biyo mu a tuwita: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel