Yanzu kalanzir da gas ya gagari talaka a Najeriya!

Yanzu kalanzir da gas ya gagari talaka a Najeriya!

Ana ci gaba da fuskantar karancin man kalanzir da kuma iskar gas a jihojin Najeriya, in da a halin yanzu ake siyar da lita guda ta kalanzir a kan Naira 300 ko fiye da haka, yayin da farashin iskar gas shi ma ya tashi sama. Rahotanni daga sassan kasar dai sun tabbatar da yadda matsalar ta jefa jama'a cikin mawuyacin hali.

Yanzu kalanzir da gas ya gagari talaka a Najeriya!
Yanzu kalanzir da gas ya gagari talaka a Najeriya!

A wani labarin kuma, Kungiyar ma'aikatan man fetur da iskar gas ta soma yajin gama-gari saboda korar 'ya'yanta daga aiki da ake yi.

Kakakin kungiyar PENGASSAN, Emmanuel Ojugbana, wanda ya shaida wa majiyar mu hakan, ya kara da cewa sun dauki matakin ne saboda kamfanonin man da suke yi wa aiki ba sa aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla kan jin dadin ma'aikata.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar CAN ta yabawa Shugaba Buhari

A cewarsa, za su tattauna da ministan kwadagon kasar Chris Ngige domin ya shiga tsakaninsu da kamfanonin man.

Yajin-aikin dai zai yi tasiri wajen hako da fitar da man fetur da iskar gas.

Kungiyoyin ma'aikatan man dai sun dade suna yajin-aiki a Najeriya, akasari domin su matsa a aiwatar da wasu matakai da suke son ganin an dauka.

Ku biyo mu a Facebook: https://web.facebook.com/naijcomhausa/

Ku biyo mu a tuwita: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel