Mataimakin gwamnan jihar Delta na rokon yan bindiga su daina kai hare-hare

Mataimakin gwamnan jihar Delta na rokon yan bindiga su daina kai hare-hare

- Mataimakin gwamnan jihar Delta, Kinglsey Otuaro, yace sulhu ne kawai zai magance rikicin Neja Delta

- Otuaro na kira ga 'yan bindiga da suka kai hare-hare kafufuwan gwamnati da sunan nuna bacin bacin ransu

Mataimakin gwamnan jihar Delta na rokon yan bindiga su daina kai hare-hare
Mataimakin gwamnan jihar Delta na rokon yan bindiga su daina kai hare-hare

Mataimakin gwamnan jihar Delta, Kinglsey Otuaro, yayi kira ga yan bindiga su share shirin cigaba da kai hare-hare kafufuwan man fetur a yankin Neja Delta.

Otuaro wanda ya kasance shugaban kungiyar Delta State Advocacy Committee Against Oil Facility Vandalism, (DSACAOFV) ya fadi a ranan Talata,10 ga watan Disamba, yace sulhu ne kawai zai magance rikicin yankin Neja Delta. Vanguard ta bada rahoto.

KU KARANTA: Fayose yace ba za'a kara kudin wuta ba

Mataimakin gwamnan yace : “ Har yanzu ba’ a gama sulhu ba, saboda haka babu bukatan kara kai hare-hare kafufuwan gwamnati a matsayin hanyan nuna bakin cikinsu."

Otuaro yana rokon yan bindiga akan barazanar da suka fara yin a cewan zasu cigaba da kai hare-hare a Neja Delta, bisa ga shawaran gwamnatin tarayya na daina tattaunawan sulhu da kungiyar Pan Niger Delta Forum, PANDEF.

Kana yan bindigan sun ce gwamnatin tarayya ta mayar da ofishin Niger Delta Development Commission (NDDC) sakatariyan All Progressives Party (APC), kuma tayi gargadi ga hukumar cewa su zasu fara kaiwa hari idan suka cigaba da hare-harensu saboda abunda suka gano abin kunya ne.

https://www.facebook.com/naijcomhausa

https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel